fbpx
Monday, October 26
Shadow

Tag: Zanga-zangar SARS

Zanga-Zangar SARS: Shugaba Buhari ya samar da Biliyan 25 dan tallafawa matasa

Zanga-Zangar SARS: Shugaba Buhari ya samar da Biliyan 25 dan tallafawa matasa

Siyasa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya samar da ware Naira Biliyan 25 dan tallafawa matasa.   Ministar kudi,  Zainab Shamsuna Ahmad ce ta bayyana haka a ganawar da ta yi da mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Balarabe a Jiya, Asabar. Tace an ware kudinne dan magance wasu daga cikin matsalolin da matasa masu zanga-zangar SARS suka yi korafi akansu. Tace dalili kenan da shugaban kasar yace kowane Minista ya je jiharsa ya tatauna da masu ruwa da tsaki da kuma matasan.   Tace nan gaba kudin zasu karu zuwa Naira Biliyan 75.
FASA MA’AJIYAR ABINCI TA HUKUMA BA DAIDAI BA NE

FASA MA’AJIYAR ABINCI TA HUKUMA BA DAIDAI BA NE

Siyasa
1. Cikin 'yan awowi kadan da suka wuce mutane sun yawaita tambayar mu game da fasa ma'ajiyar abinci na taimakon Corona da aka a wasu jihohi, da kuma diban abincin, ko saye a hannun wanda ya diba. 2. Amsarmu ga masu wannan tambayar ita ce dukkan abin da aka tambayar ba daidai ba ne musulmi ya yi shi: Kada ku fasa shagunan gwamnati, kada ku dauki abincin da aka ajiye a cikin shagunan, kada ku saya ko ku sayar da irin wannan abincin.   3. Lalle bin doka da oda yana daga cikin abin da zai tabbatar wa al'umma babbar maslaharsu da kuma maslahar kasarsu.   4. Sannan muna kira ga hukumomin da abin ya shafa su dauki matakin gaggawa domin gyara inda suka yi kure domin samar wa Kasa da talakwan kasa mafita mai kyau. Allah ya taimake mu. Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
Bani da hannu a korar Inyamurai, Inji Farfesa Soyinka, Gwamnatin jihar Legas ma ta cewa Inyamuran su kwantar da hankulansu

Bani da hannu a korar Inyamurai, Inji Farfesa Soyinka, Gwamnatin jihar Legas ma ta cewa Inyamuran su kwantar da hankulansu

Siyasa
Bayan fitowar shugaban wata kungiyar Yarbawa ta Young Yarbawa ta Yoruba For Freedom, Adeyinka Grandson yace Inyamurai su fita daga kasar Yarbawar nan da ranar Litinin ko su fuskanci Wilakanci, kungiyoyi da dama sun fito sun karyatashi.   Da farko dai shahararren Marubuci, Farfesa Wole Soyinka ya bayyana cewa wasu kalamai da aka yi amfani dasu a cikin barazanar da Adeyinka ya fitar ana dangantashi dasu ba gaskiya bane.   Yace kalaman da ake cewa wai ya bayyana abinda Hausawa da Yarbawa da Inyamurai suke so an dade da yinsu shekaru aru-aru kuma tun a wancan lokacin ya fito ya karyatasu yace bashi ya fada ba, yace da zai so yayi watsi da wadannan maganganu amma yanda kasar ta dau zafi yasa dole ya fito yayi Magana.   Yace wadannan matasa suna satar sunanshi ne...
Wani Bayerabe yace sun baiwa Inyamurai nan da zuwa Gobe Litinin su bar kasar Yarbawa ko kuma su dandana kudarsu

Wani Bayerabe yace sun baiwa Inyamurai nan da zuwa Gobe Litinin su bar kasar Yarbawa ko kuma su dandana kudarsu

Siyasa
Wani bayerabe me suna Adeyinka Grandson ya garhadi Inyamurai dake zaune a Kasar Yarbawa su bar kasar Yarbawa din nan da zuwa Gobe Litinin.   Tun a ranar Juma'a ne ya fitar da sanarwar inda yace sun yiwa Inyamuran Adalci sun basu nan da awa 48 su bar kasar Yarbawa su koma garuruwansu. Yace idan Litinin ta zo zaau tare hanya zasu ahiga ma'aikatu da guraren kasuwanci dan zakulo duk wanda bai ji wannan gargadi ba kuma abinda zasu musu sai ya fi na wanda aka musu a Ore, Ondo, watan Augusta na shekarar 1967.   Saidai wannan magana tashi ta jawo cece-kuce inda cikin wanda suka mayar masa da martani hadda hadimin shugaban kasa, Kayode Ogunda misi.   Yace wanna mutumin dake magana mazaunin kasar Ingila ne kuma 'yansanda ma na nemansa Ruwa a jallo saboda laifi...
Yanzu-Yanzu: Yan sanda sun dakile wani yunkuri na wawushe rumbun ajiyar kaya a Abuja, FCT

Yanzu-Yanzu: Yan sanda sun dakile wani yunkuri na wawushe rumbun ajiyar kaya a Abuja, FCT

Siyasa
Yan sandan Babban Birnin Tarayya, FCT, na Rundunar 'Yan Sandan Najeriya sun dakile wani yunkuri da wasu matasa suka yi na kutsawa cikin rumbun ajiyar kayayyakin da ke gidan al'adu a yankin 10, Garki. Matasan, wadanda yawansu ya haura 40 sun mamaye yankin ne a safiyar ranar Asabar kuma suka yi kokarin samun damar shiga cikin ginin don kwashe kayan agaji da aka ajiye a wurin na Babban Birnin Tarayya FCTA. Rundunar 'yan sanda na wurin don tarwatsa su da bindigogi da kuma hayaki mai sa hawaye. Jaridar Vanguard ta tattaro cewa dakin ajiyar da aka ce yana dauke da ruwan kwalba ne kawai kamar yadda aka an riga an rarraba sauran kayan. Kodayake, ba a yi kokarin kutsawa cikin rumbunan na Kubwa ba, bayanai sun nuna cewa ginin a halin yanzu babu komai saboda an riga an rar...
Bidiyon yanda dan sanda ke baiwa gurgu kayan Tallafin Coronavirus/COVID-19 da aka wawushe a Calabar

Bidiyon yanda dan sanda ke baiwa gurgu kayan Tallafin Coronavirus/COVID-19 da aka wawushe a Calabar

Siyasa
A jiyane Labarai suka watsu cewa matasa a jihar Cross-River suma kamar takwarorinsu na Legas da Kwara da Ogun dun gano inda ake ajiye da kayan abinci na tallafin Coronavirus/COVID-19 da aka bayar a rabawa mutane.   Sun fasa dakin abincin inda suka daka masa wawa. A wani Bidiyo da ya watsu sosai an ga wani dansanda yana taimakawa yana baiwa wani gurgu abincin da aka kwaso.