fbpx
Monday, August 15
Shadow

Takaitaccen Tarihin Masanin Tafsirin Kur’ani Sheik Dahiru Bauchi, Bayan Cikarsa Shekaru 95 Da Haihuwa

Daga Babangida A. Maina

Shahararren Malamin addinin Musulunci nan kuma daya daga cikin Khalifofin Shehu Ibrahim Inyass, wato Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya cika shekaru 95 cif da haihuwa.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi, malamin addinin Musulunci ne kuma jigo a Darikar Tijjaniyya na Afrika, bayan haka dattijo ne mai shekaru a duniya kuma mataimakin shugaban kwamitin koli na kungiyar malaman da ke bayar da fatwa a addinin Musulunci a Najeriya.

A shekarar 2019 wata hira da ya yi da dan jaridar jaridar The Punch, Armstrong Bakam, Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana wasu abubuwa dangane da rayuwarsa.

Da yake amsa tambaya a kan yadda ya zama babban malamin Tijjaniya, Sheikh Bauchi ya bayyana cewa, “ni bafulatani ne da aka haifa ranar 28 ga watan Yuni na shekarar 1927 a garin Nafada (da yanzu ke jihar Gombe), amma ni dan asalin garin Kwankiyel ne da ke karamar hukumar Darazo a jihar Bauchi.

“Na yi dukkan karatuna na addini a karkashin kulawar mahaifina, har na haddace Qur’ani, kuma ta hannunsa ne na karbi darikar Tijjaniya. Shi mahaifina ya karbi darikar Tijjaniya ne ta hannun wani mutum mai suna Alhaji Gwani Abba.

“Daga baya sai mahaifina ya bani izinin na tafi duk inda nake so domin zurfafa ilimina na addini da haddar Qur’ani mai girma.

Shehin malamin ya zama masanin tafsirin Alkur’ani mai girma wanda ya samu lambobin yabo a wannan ɓangaren, ya kuma samu digirin girmamawa a bangarori daban-daban a najeriya sama faɗin duniya baƙi ɗaya. Ko a karshe shekaran data gabata wata gidauniya ta bashi lambar yabo da kuma babban jami’in tarayya dake garin lafia jihar Nassarawa sun bashi lambar yabo ta gigirin girmamawa.

Karanta wannan  Koulibaly ya haskaka yayin da Chelsea ta raba maki da Tottemham bayan sun tashi wasa da kunnem doki 2-2

Kadan daga cikin irin nasarorin da Shehu Dahiru Usman Bauchi ya samu a tsawon shekaru sa.

* Ya musuluntar da dubban mutane a wurin addinin musulunci a hannun sa.

* Shehi a duk lokaci bayan lokaci yana karanta Alkur’ani kuma sai yayi saukar Alkur’ani a kwana biyu.

* Shehi ya bada lazumin Darikar Tijjaniyya wa dubban mutane da dama a fadin duniya.

* Mutane fiye da 40,924 suka haddace Alqur’ani mai girma a makarantun sa dake fadin Najeriya.

* Shehun malamin ya kafa makarantun haddar Alqur’ani guda 383 a najeriya dama Afrika.

* Karkashin gidauniya sa an gina dakunan karatu guda 33,060 A arewacin najeriya.

* Allah ya bashi yara mahaddata Alkur’ani mai girma kusan 76 a duniya tare da jikokin sa mahaddata 200, tattaba kunne fiye da 15. Duk mahaddata Alkur’ani mai girma.

* Ya yaye dalibai a makarantun sa fiye da 50,400 mahaddata da kuma dalibai masu neman haddaci Alkur’ani kusan 90,500.

Shehu Dahiru yana da mata guda hudu da yaya da dama a raye tare da kuma jikoki da tabbata kunne da dama a duniya.

Allah ya kara lafiya rayuwar sa albarka, ya kara tsawon shekaru masu albarka. Allah ya kara lafiya da nisan kwana. Amiin

Daga: Babangida Maina
Founder MD/CEO Tijjaniyya Media News

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.