fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Takarar shugabancin kasa ta Goodluck Jonathan a APC na samu koma baya

A yayin da ake ci gaba da tuntuba kan yanda tsohon shugaban Najeriya,  Goodluck Jonathan zai yi takarar shugaban kasa a shekarar 2023 a jam’iyyar APC.

 

Wasu masu goyon bayan ‘yan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar sun nuna basa son wannan magana kuma basa goyon bayanta.

 

Daga ciki, magoya bayan mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da magoya bayan Tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmad Tinubu sun bayyana cewa basa goyon bayan wannan lamari.

 

Ana dai ta samun karuwar wanda basa goyon bayan a baiwa Goodluck Jonathan takarar jam’iyyar ta APC a 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published.