Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya sauka a Asaba bayan dawowarsa daga babban birnin tarayya biyo bayan zabar shi da Atiku yayi a matsayin abokin takararsa.
Inda dumbin mutane suka taru suna taya shir murnar zama abokin takarar Alhaji Abubakar dake neman takarar shugabancin Najeriya a tutar PDP.
Okowa ya hallaci wurin ne tare da matarsa inda ya bayyana masu cewa talaka zai sha jar miya idan har aka zabe Atiku a matsayin shugaban kasar Najeriya.
Kuma yace Alhaji Abubakar nada burin gina kasar ta bangarori daban daban kama daga harkar kasuwanci dama ayuuka bakidaya.