fbpx
Monday, June 27
Shadow

TALLAFI : Wike Ya Taimaki Karamar Hukumar Birnin Gwari Jihar Kaduna

Daga Yahaya Abdullahi Birnin Gwari

Mai Girma Barista Ezenwo Nyesom Wike, Gwamnan Jihar Rivers, kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya bada gudummawar kayan abinci don tallafa wa ‘yan gudun hijiran da ‘yan fashi da makami, da masu garkuwa da mutane suka tilasta masu barin muhallansu don su tsira da ransu.

Kayan gudummawar sun hada da; masara, shinkafa, taliya, gishiri, turamen zannuwa, sabulun wanki da bokitai. Yanzu ake hada su. Da zaran sun hadu za a tsara rabo yadda kayan za su kai hannuwan wadanda suka cancanta. Da zaran an bada izini, za a raba su ga ‘yan gudun hijiran.

Leave a Reply

Your email address will not be published.