fbpx
Monday, August 15
Shadow

Tankar danyen mai ta babbake tare da mutane uku a jihar Kogi

Tankar danyen man fetur ta babbake tare da mutane uku a jihar jihar Kogi da misalin karfe takwas na dare ranar litinin.

Lamarin ya faru ne a babban hanyar dake babban birnin jihar Kogi watau Lokoja bayan da birke ya kwacewa wani direban babban mota ya afkawa dan ‘uwansa daya faka mota a gefen titin.

Wanda hakan yayi sanadiyar rayuwar mutane uku kuma wasu mutane biyu suka samu raunika.

Inda hukumar dake lura da ababen hawa akan hanya ta FRSC ta tabbatar da faruwar wannan hadarin ranar talata kuma tace an kai wa’yanda suka ji raunin asibiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published.