Motocin dakon man fetur 11 sun kone a ranar Talata lokacin da gobara ta kama wani garejin ajiye motoci a Anguwan Mu’azu a Kaduna.
Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA), Abdulahi Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Shugaban KADSEMA, wanda ya je wurin domin tantance yadda barnar ta kasance, ya ce lamarin gobarar ya haifar da gano wasu ayyukan bata gari da suka hada da kayayyakin mai a yankin.
Ya ce hukumar za ta binciki sa hannun mazauna garin da kuma mambobin kungiyar a cikin irin wadannan ayyukan da ake zargin sun haifar da tashin gobarar.
Shaidun gani da ido sun sanar cewa wasu mutane kalilan sun samu raunuka kuma an garzaya da su asibiti don kulawa.