fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Tarzoma ta barke tsakanin ‘yan Boko Haram suna ta kashe junansu

Mayaƙan ISWAP da na Boko Haram ɓangaren Abubakar Shekau sun yi mummunan artabu da juna kan iko da wani yanki a Tafkin Chadi.

Jaridar PRNigeria ta ce ƴan ta’adda aƙalla 54 aka kashe cikin wata ɗaya a artabu tsakanin mayaƙan ISWAP da na Boko Haram ƴan ƙabilar Buduma a Jamhuriyyar Nijar.

A cewar jaridar ƴan Boko Haram daga ƙabilar Buduma suka fara kai wa ISWAP harin ba-zata a ƙauyen Chikka da ISWAP ke iko da shi a ranar 3 ga watan Maris domin kwasar ganima.

“Mayaƙan daga ɓangaren Shekau sun mamaye ƙauyen inda suka kashe ƴan ISWAP da dama tare da sace matansu guda biyar. Kuma mayaƙan sun saci kayayyakin abinci kafin su gudu a cikin dare.”

Karanta wannan  Allah ne ya umurce ni na boye su a cikin coci har sai Yesu ya dawo karo na biyu, cewar faston da aka kama yayi garkuwa da mutane 77 a jihar Ondo

Daga baya kuma ISWAP ta kai harin ramuwar gayya inda suka yi ɓarin wuta da ƴan Boko Haram a yankin Kaduna Ruwa da Kaiga kuma an yi hasarar rayuka daga ɓangarorin biyu, a cewar jaridar.

Sannan kuma mayaƙan Boko Haram sun kashe wasu makiyaya 22 tare da sace shanunsu saboda sun biya haraji ga ISWAP maimakon ɓangaren Shekau. Sun kuma abka wa wani kwale-kwalen da ke ɗauke da makamai na ISWAP inda suka kashe mayaƙa takwas suka kwashe makaman da ke cikin kwale-kwalen.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.