fbpx
Friday, July 1
Shadow

Taufa!: Wanda suka sha Rigakafin Coronavirus/COVID-19 a kasar Australia na nuna cewa sun kamu da cutar Kanjamau

Kasar Australia ta soke yunkurin sayen rigakafin cutar Coronavirus/COVID-19 na Dala Miliyan 750 daga wani kamfani, bayan da rigakafin ya rika nuna sakamakon karya na cewa wanda suka shashi sun kamu da cutar Kanjamau.

 

Wadanda suka bada kansu aka yi gwajin maganin sun rika nuna sakamakon kamuwa da cutar kanjamau amma da bincike yayi zurfi sai ala gane cewa ba da gaske bane. Saidai duk da haka an dakatar da amfani da rikagafin, kuma shine rigakafin Coronavirus/COVID-19 na farko a Duniya da ba’a yadda dashi ba, kamar yanda New York York times taruwaito.

 

Firaiministan kasar Scott Marrison ya bayyana cewa amma zasu biya kamfanin diyyar rigakafin da suka yi Alkawarin saye.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.