Manajan kungiyar Manchester United Ole Gunnar yana so ya karawa kungiyar su karfi ta bangaren gaba a kasuwar yan wasan kwallon kafa mai zuwa kuma yana da ra’ayin siyan Jack Grealish daga kungiyar Aston Villa.
Aston Villa sune na 19 a teburin gasar premier lig amma duk da haka Jack Grealish yayi nasarar jefa kwallaye har guda tara kuma ya taimaka wurin kwallye guda takwas a wasanni guda 31 daya buga a wannan kakar wasan.

Jack Grealish ya bayyan cewa yana kwaikwayon tsarin yadda tauraron Portugal Cristiano Ronaldo yake yin wasa, ya kara da cewa ba wai yana nufin ya kusa kamo Ronaldo bane, kawai yana kokarin bin tsarin zakaran dan wasan ne saboda yana son shi kuma yana kallon wasanni shi sosai.
Kokarin da Jack Grealish yake yi a wannan kakar wasan yasa United sun fara ra’ayin siyan dan wasan yayin da kungiyar shi ta sa mai farashin euros miliyan 80, kwantirakin da Aston Villa suka yiwa Grealish ba zai kare ba sai nan da 2023.