Tauraron dan wasan Najeriya kuma tsohin kaftin dinta, Mikel Obi ritaya daga wasan Tamola.
Dan wasan Najeriya yayi nasarar lashe kofuna a wasan tamola hadda na zakarun nahiyar turai a shekarar 2012 a kungiyar Chelsea dama wasu kofunan.
Kuma kafin ritayar tasa ya tala leda ne da kungiyar Kuwait.
Obi ya bayyana ritayar tasa ne a shafinsa na Instagram inda mika sakon godiyarsa ga kocawansa da kungiyoyi da abokan aiki dama masoya bakidaya.