Tauraruwar Fina-finan Hausa, Hafsat Idris, wadda aka fi sani da Barauniya, ko kuma ‘yar Fim, tawa diyarta me suna Khadija Aure.
Abokan aikinta, da ‘yan uwa da dama sun taru wajan kayataccen bikin da aka yi inda suka tayata Murna da farin ciki.
Hafsat ta saka hotuna da Bidiyon bikin sosai a shafukanta na sada zumunta. Itama abokiyar aikinta, Saratu Gidado, wadda aka fi sani da Daso, ta saka hotunan a shafukanta inda ta bayyana cewq wajan bikin diyar Hafsat Idris ce me suna Khadija.
Da yawa dai sun rika mamakin hakan inda suka rika tambayar Daso cewa shin diyar Hafsat Idris ce ta cikin ta ko kuwa yaya batun yake?
A wasu lokutan dai Daso ta bayar da amsar cewa Eh! Diyar Hafsat ce, a wasu Lokutan kuma tace su tambayeta.
https://www.instagram.com/p/CM6X3SYJ3m5/?igshid=9s2m4a6rnplg





A baya dai, hutudole.com ya ruwaito muku yanda Aljanun Maryam Waziri da aka fi sani da Laila a cikin shirin fim din Labarina suka tashi.
Karin sanannun fuskokin da suka halarci wannan biki sun hada da diyar tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu, Sarki, Watau Fatima, Sadiya Gyale da Hadiza Kabara da sauransu.