fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Tawagar Banza da Wofi shugaba Buhari ya aika Sokoto, zuwa zasu yi su sha shayi su dawo>>Dawisu

Tsohon hadimin gwamnan jihar Kano, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana tawagar da shugaba Buhari ya aika Sokoto da cewa ta banza da wofi ce.

 

Salihu ya bayyana haka a shafinsa na sada zumunta inda yace shi shugaba Buhari kullun baya yin abu dan kashin kansa, sai an caccakeshi.

 

Yace tawagar ma babu abinda zata yi, ta banza da wofi ce, shayi kawai zasu su sha, kamin a sake kai wani harin.

Shugaba Buhari dai ya aike da tawaga ta musamman jihar Sokoto saboda harin da aka kai da ya kashe mutane 42 wanda akawa kisan gilla.

Karanta wannan  Majalissar dinkin duniya tace harkar Crypto zata iya rusa Najeriya da sauran kasashen da suka cigaba

 

Dawisu ya sha caccakar masu rike da mukamai, wanda kusan hakane yasa ya rasa aikinsa na hadimin gwamnan Kano.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.