Tsohon tauraron dan wasan kwallon kafa, Thierry Henry kenan sanye da kayan al’ada na inyamurai, tauraron dan kwallon yazo Najeriya dazu da yamma domin ya kayatar da abokan huldar kamfanin giya na Guinness.
Yayi tashe sosai a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal. Kuma shine dan wasan da yafi kowane dan wasa ciwa Arsenal din kwallaye, har yazu babu wanda ya kamoshi.