fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Thomas Muller: Lewandowski yafi Cristiano Ronaldo a yanzu

An tambaya tauraron dan wasan tsakiya na kungiyar Bayern Munich Thomas Muller cewa tsakanin Cristiano da Messi waye yake so yayi aiki tare da shi?. Muller ya yaba tauraron Barcelona Messi da zakaran Juventus Cristiano kuma yace su kwararrun yan wasan ne.

Daga bisani kuma yace yafi so ya yayi aiki tare da abokin aikin shi Lewandowski wanda yanzu tauraron shi yake haskakawa a nahiyar turai yayin yafi gabadaya sauran yan wasan kwallon kafa yawan kwallaye a wannan kakar wasan.
Muller yace a lokacin daya fara buga wasan kwallonkafa yafi so yayi aiki tare da Messi saboda a lokacin ana bashi kwallo shi kuma yaci. Amma a yanzu daya kware, shi ke baiwa wasu kwallon domin su ci kuma zai fi son yayi aiki tare da dan wasa kamar Ronaldo.
Amma su yanzu a Bayern Munich suna da lewan-goals-ki!, kuma a tunanin shi yafi Cristiano Ronaldo a yanzu.
Muller ya taimaka wurin cin kwallaye guda har guda 18 a gasar Bundlesliga yayin da shi kuma Lewandowski yayi nasarar cin kwallaye guda 29 a wannan kakar wasan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.