fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Tikitin Musulmi da Musulmi: Osinbajo yayi tsokaci kan neman izinin shugaba Buhari ya bashi damar ficewa daga APC

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, farfesa Yemi Osinbajo yayi tsokaci kan rahotannin dake bayyana cewa ya nemi izini wurin shugaba Buhari na barin APC.

Inda farfesan yace karya ake yi masa shi bai nemi izinin ficewa daga jam’iyyar ba, mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar Akande ne ya bayyana hakan.

Rahotanni da dama sun bayyana wannan labarin cewa ya nemi izinin barin jam’iyyar saboda ta tsayar da Musulmi da Musulmi a matsayin ‘yan takararta na shugaban kasa.

Amma yanzu ya karya wannan rahoton yace labarin kanzan kurege ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published.