fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Tinubu ba ruwanshi da mulkin Buhari domin ko kwangila basu taba bashi ba, saboda haka kar wani ya dora masa laifi, cewar Oshiomole

Tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole ya bayyana cewa babu ruwan Bola Ahmad Tinubu da mulkin shugaba Buhari domin ko kwangila basu taba bashi ba,

Sannan Asiwaju bai taba rike wani mukami a mulkin shugaba Buhari ba, saboda haka kar wani ya dorawa dan takarar shugaban kasar na APC laifi.

Tsohon shugaban jam’iyyar ta APC ya bayyana hakan ne a safiyar yau Laraba yayin dayake ganawa da manema labarai na Arise TV.

‘Yan kasar Najeriya yawancinsu na cewa shugaba Buhari bai cika alkauran daya yi masu ba a mulkinsa, wato magance matsalar tsaro, samar da ayyuka da kuma yaki da cin hanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published.