fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Tinubu da Shettima sunci zabe sun gama, cewar Simon La Long

Gwamnan jihar Filato, Simon La Long, wanda ya kasance babban darekta na yakin neman zaben Tinubu ya bayyana cewa babu shakka APC ce zata yi nasarar lashe zabe mai zuwa.

Shugaban tsaron La Long Yakubu Dati ne ya wakilci uban gidan nasa ya bayyana hakan a taron da kungiyar mabiyan Tinubu ta gudanar a babban birnin tarayya Abuja.

Inda yace ganin yadda APC ta shahara dama su kansu yan takarar nata hakan na nuna cewa sune zasu lashe zaben na shugaban kasa da za a gudanar a shekara mai zuwa.

Karanta wannan  Kasar Cuba ta halatta auren jinsi

Kuma ya jinjinawa kungiyar ta BAT dake yiwa Tinubu yakin neman zaben inda yace kamata yayi gabadaya masoyan APC duk su fito domin kada kuru’unsu a ranar zabe.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.