Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal ya bayyana cewa bai ji dadin maganar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya yi ba akan shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Bola Tinubu ya bugi kirjin cewa, shine ya taimakawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya ci nasarar zabe a shekarar 2015 amma gashi yanzu yana son cin amanarsa.
Saidai Babachir David Lawal yace goyon bayan bayerabe a kasa yana da matsala saboda zasu sa mutum a rika ganinshi kamar yana cin amanar mutanensa ne.
Yace ba Tinubu kadai bane ya taimakawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba wajan nasarar zabe a shekarar 2015.
Yace amma sauran duk basa surutu irin wanda Tinubun ke yi.