Kungiyar masoyan Tinubu ta kudu masu yammacin Najeriya, SWAGA ta bayyana cewa APC zata tafka babban kuskure idan har bata tsayar da Tinubu a matsayin dan takararta ba.
Inda kungiyar tace Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ne kadai dan karar da zai iya karawa da Atiku a APC kuma har yayi nasarar kayar da shi.
A karshe kungiyar tace idan har APC ta tafka kuskure taki zabar Tinubu a matsayin dan takararta to lalulube zatayi cikin duhu a zaben shekarar 2023.