fbpx
Saturday, September 23
Shadow

Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN Emefiele, kuma DSS sun kamashi

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin ƙasar – CBN Godwin Emefiele daga muƙaminsa.

Sanarwa daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayyar ƙasar ta ce an dakatar da gwamnan CBN ne domin a gudanar da bincike sannan kuma ya sauya fasalin harkokin kuɗi a ƙasar.

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban banki, Mr Godwin Emefiele, CFR daga ofis ba tare da bata lokaci ba,” in ji sanarwar.

An umurci gwamnan CBN din ya mika ragamar tafiyar da harkokin ofis din ga mataimakin gwamna mai kula da harkokin gudanarwa wanda zai kasance mukadashin gwamna har sai an kammala bincike da kuma sauye-sauye a bangaren kuɗi.

Matakin da shugaba Tinubu ya dauka na zuwa ne kasa da mako biyu da aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasar.

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ne ya naɗa Emefiele a matsayin shugaban CBN a shekara ta 2014.

Sai dai wasu matakai da ya ɗauka gabanin babban zaɓen Najeriya na 2023 ya janyo ce-ce ku-ce mai yawa a ƙasar.

Batun sauya fasalin kuɗi da bankin ya ƙaddamar ya haifar da ƙarancin kuɗi a hannun al’umma, wani abu da ya janyo wahalhalu da dama.

Sai dai Emefiele ya ce sauya fasalin kuɗin wani yunƙuri ne na yaƙi da rashawa da matsalar tsaro da kuma ɗabbaƙa tsarin rage amfani da tsabar kuɗi tsakanin al’umma.

Amma lamarin bai yi wa Bola Tinubu daɗi ba, wanda a lokacin yake takarar shugaban ƙasa.

Wasu daga cikin na kusa da shugaban na yanzu sun yi zargin cewa sauya fasalin kuɗin wani yunƙuri ne na yin zagon-ƙasa ga nasararsa a zaɓen.

Hakan ne ma ya sa ake ganin labarin dakatar da Godwin Emefiele ba zai zo wa mutane da dama da mamaki ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *