Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya gana da masu hannu da tsaki na jam’iyyar tasu a sirrince ranar talata.
Wanda suka hada da gwamnan jihar Kaduna, wanda ake rade raden cewa yana fushi da Tinubu saboda bai zabe shi a matsayin abokin takararsa ba,
Sai gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, abokin takarar Tinubu Kashim Shettima, taohon shugaban APC Adams Oshiomole, gwamnan Zamfara Bello Matawalle da kuma tsohon sakataren APC Iyiola Omisore.
Sun gudanar da taron ne a gidan Tinubu dake babban birnin tarayya kuma duk da cewa ba a san asalin abinda suka tattauna a taron ba,
An samu labari daga majiya mai karfi cewa har yanzu dai kan zabar Musulmi daya yi ne a matsayin abokin takararsa da kuma zabar gwarzon da zai iya yi masa shugabanci a kungiyar kamfe dinsa nan da watan satumba.