Tinubu Ya Gwangwaje Ɗariƙar Tijjaniyya Da Kayataccen Gida A Abuja
Daga Imam Aliyu Indabawa
Wannan shi ne sabon gida da Shugaban ƙasa mai jiran gado Bola Ahmad Tinubu ya yi kyautarsa ga ƙungiyar Ansaruddeen Tijjaniyya a matsayin hedikwata.
Shugabannin ƙungiyar daga sassa daban-daban ne suka halarci bikin miƙa sabon gidan a jiya a babban birnin tarayya Abuja.