fbpx
Friday, August 12
Shadow

Tinubu ya hayo fastocin da ba a san su ba sun hallacci taron kaddamar da Kashim Shettima

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad ya kaddamar da tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa yau ranar laraba.

Inda yayi burus da caccakara da ake yi na cewa ya zabi dan uwansa Musulmi a madadin ya zabi Kirista saboda ayi adalci.

Kuma a taron wanda yanzu haka suke kan gudanarwa anga wasu fastoci sun zo wanda ba a san su ba suma sun hallaci taron.

Tinubu ya hayo fastocin ne don ya sanyaya zuciyar Kiristocin kasar dake sukarsa saboda ya nuna son kai, amma yace ba son kai bane cancanta ce tasa yayi hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published.