fbpx
Friday, August 12
Shadow

Tinubu ya sasanta da sanatocin APC sun fasa sauya sheka, cewar Kashim Shettima

Tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Tinubu ya magance matsalar da sanatocin jam’iyyar ke fuskanta.

Inda yace shi ya jagorancisu suka je wurin Asiwaju Bola Tinubu a babban birnin tarayya Abuja ranar lahadi.

Kum ya bayyana bayan taron cewa Tinubu ya roqe su dasu cigaba da siyasarsu a jam’iyyar ta APC kuma sun amince.

Domin har sun sha alwashin cewa zasu taimakawa jam’iyyar dari bisa dari don ta lashe zaben shekarar 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published.