fbpx
Friday, August 12
Shadow

Tinubu ya tsige ni a cikin kungiyar da zata yi masa yakin neman zabi saboda na janyewa Osinbajo, cewar tsohon dan takarar shugaban kasa

Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Dr. Nicholas Felix ya bayyana cewa Tinubu ya cire shi a cikin kungiyar da zata yi masa yakin zabe.

Nicholas ya bayyana hakan ne makonni uku bayan an gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam’iyyar APC.

Inda kafin zaben ya goyi bayan Osinbajo har ya janye masa a farfajiyar zaben, amma a karshe Tinubu ne yayi nasarar lashe zaben.

Wanda yanzu hakan yasa Tinubu ya tsige shi a cikin kungiyar da zata yi masa yakin neman zabe, kuma Felix ya koka akan hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published.