fbpx
Monday, August 15
Shadow

Tinubu ya yiwa babban abokinsa kuma mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo fatab samun sauki kan tiyatar da aka yi masa

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola ahmad Tinubu ya yiwa babban abokinsa Osinbajo fatan samun sauki kan tiyatar da aka yi masa.

Tinubu ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter, inda yace yana yiwa babban abokin basa fatan samun sauki kan tyatar da aka yi masa a kafa.

A ranar asabar din data gabata ne aka yiwa Farfesa Osinbajo tiyata a kafarsa bayan ya samu rauni a wasan kwallo na squash.

Kuma anyi masa tiyatar ne a gida Najeriya a Ikeja dake jihar Legas, wnda yasa kungiyar likitoci ta jinjina mas da bai fita waje neman lafiya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.