fbpx
Friday, August 12
Shadow

Tinubu zai iya daga darajar naira ta koma daidai da dalar Amurka

Ayodele Adewale, shugaban karamar hukuma a jihar Legas ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu zai iya daga darajar naira ta koma daidai da dala.

Ya bayyana hakan ne yayin dayake ganawa da manema labarai na ranar laraba.

Inda yace Tinubu babban dan siyasa ne kuma zai iya kawo manyan ‘yan kasuwa su saka hannun jari a Najeriya wanda hakan zai habbaka tattalin arzikin kasar.

Sannan kuma yace abokin takararsa Kashim Shettima shima zai bayar da gudun mawa sosai, kuma kasancewar Musulmai bai kamata ya kawo cece kuce a kasar ba cancanta ce tasa APC tayi hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published.