fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Tinubu zai yi nasara da kashi 60 cikin 100 a zaben 2023 – Okechukwu

Darakta-Janar na Muryar Najeriya (VON) kuma mamba a jam’iyyar APC mai mulki, Osita Okechukwu, ya yi hasashen cewa mai rike da tutar jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a babban zaben shekara mai zuwa zai samu nasara da Kashi 60 cikin dari.

Ya yi wannan hasashen ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja.

Da yake jawabi akan dan takarar jam’iyyar a zaben shugaban kasa da za’a yi a watan Fabrairun 2023, Okechukwu ya jaddada cewa jam’iyyar APC za ta lashe zaben da kashi 60 cikin 100 a kan sauran abokan hamayyarsa.

Karanta wannan  Mutane miliyan daya muka kashe domin a samu zaman lafiya a Najeriya, cewar shugaba Buhari

Ya kara da cewa; Jihohi 22 na kasar suna karkashin jami’iyyar APC Kuma ko a Majalisar Dokoki ta kasa suke da rinjaye.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.