TO FA: Dan takara ya kwace motocin da ya rabawa deligate bayan ya fadi zaben fidda gwani a PDP
Muryoyi ta ruwaito Rahotanni na nuna cewa dan takarar Sanata dake wakiltar mazabar Ondo Central, Ayo Akinyelure ya kwace kyautar motoci da yayi wa deligate ko jagorori da jiga-jigan jam’iya bayan da ya fadi zaben fidda Gwani na PDP.
Ana dai ta cece kuce kan wannan lamari kodayake kakakin dan takarar yace ba duka suka kwace ba ‘an karbi na wani jigon jam’iyar PDP ne da saboda rawar da ya taka wajen faduwar Dan takarar’
Shin kwace motar ya dace?
Idan kana cikinsu zaka maida motar?