fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Tonin Silili: Tinubu ya taba bayyana cewa bai kammala makarantar sakandiri ba saboda basu da kudi

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu yace an sace masa takaddun makarantarsa ne lokacin mulkin soja.

Inda Tinubu ya baiwa INEC Affidavit a madadin takadddun makarantar nasa inda yace yayi karatun sakandiri ne a Ibadan sai kuma jami’ar Chicago.

Amma yanzu an samu rahotanni sun bayyana cewa Tinubu baiyi jami’ar ta Chicago ba wadda ya cewa hukumar zabe ta INEC yayi, Sahara Reporters suka bayyana.

Sannan kuma dan takarar shugaban kasar ya taba bayyana cewa yayi makarantar firamari amma bai kammala sakandiri ba saboda basu da kudi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.