fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Tonon Silili: An gano Biliyan 58 da aka kashe kan ayyukan da babu su a zahiri a karkashin Mulkin Buhari

Kungiyar BudgIT dake saka ido kan yanda ake gudanar da ayyukan gwamnati tace ta gano Naira Biliyan 58 da aka ware da sunan cewa za’a yiwa Al’umma aiki, amma a zahiri, ba’a ga inda aka yi wadannan ayyukan ba.

 

Me kula da yada labarai na kungiyar, Iyanu Fatoba ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

 

Yace daga cikin kudin akwai Naira Miliyan 250 da aka ware dan taimakawa wasu mutane a Arewa wajan sayen injin Nika, Mashina, keken dinki da sauransu amma babu inda aka ga anyi wannan rabo.

 

Yace akwai kuma Biliyan 28 da aka ware a ma’aikatar Noma wadda itama akayi walle-walle da ita.

Karanta wannan  Najeriya zata iya lalacewa idan kuka cigaba da sukar mulkina, cewar shugaba Buhari

 

Yace akwai kuma wata Biliyan 4.8 da itama aka warewa wasu yankunan Najariya amma ba’a san ina kudin suka yi ba.

 

Yace akwai kuma Biliyan 13 da aka warewa ofishin sakataren gwamnatin tarayya wanda a zahiri bashi da wani aiki da ya wuce tallafawa jama’a amma ba lallai tallafin na kaiwa garesu ba.

 

Kungiyar tace muddin ana kin gayawa mutane yanda aka yi da kudadensu to akwai wahalar bibiyan ba’asin kudin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.