An zargi Sanata Danjuma Usman Shiddi da safarar makamai.
Saidai Sanatan da ya fito daga jihar Taraba ya musanta wannan zargi da ake masa.
Wasu labarai dake yawo a kafafen sada zumunta sun bayyana cewa, an kama motar sanatan makare da makamai.
Saidai a jawabin da ya fitar ranar Lahadi, Sanatan yace wannan zargi da ake masa ba gaskiya bane.
Yace ana yayata wannan maganane kawai dan a bata masa suna.