Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya saka agogon kasaita ta naira miliyan 455 a ziyarar daya kaiwa shugaba Buhari a Daura.
Gwamnan yana daya daga cikin gwamnonin da shugaban gwamnonin APC, Atiku Bagudu ya jagoranta suka kaiwa Buhari ziyara a Daura.
Wani ma’aikacin dake gina gidaje ne ya bayyana hakan cewa kudin agogon zai iya ginawa dalibai gini mai ajujuwa shida a cikinsa sau 74 amma banda kudin fili.
Kuma kudin zasu iya gina asibitoci kusan talatin kan naira miliyan 15 a kowane gini guda. Dalibai da dama suna fama da matsalar ajujuwa da kuma karancin bencina makarantun su na jihar.