A yayin da aka kama hanyar fita daga watanni 3 na 2 na shekarar 2021, wanda a turance ake kiransu da quarters, an gano cewa cikin kudin da gwamnatin tarayya ta warewa tsarin NYIF, Biliyan 12.3, Biliyan 3 kacal aka baiwa matasa.
Ma’aikatar matasa da wasanni ta samu amincewar Majalisar Zartaswa da CBN kan baiwa matasa Biliyan 12.5 a karkashin tsarin.
Amma zuwa yanzu Biliyan 3 kacal aka baiwa matasa ta hannun bankin NIRSAL, kamar yanda jaridar Leadership ta gano.
Saidai a nata bangaren, ma’aikatar matasa da wasanni ta sanar da cewa, matasa 5,200 ne aka baiwa Biliyan 1.6 zuwa yanzu.