fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tonon Silili: Gwamnatin tarayya ta bayyana sunayen masu kai hare-hare Arewa

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, Kungiyar Boko Haram data ‘yan Bindiga ne suka hada kai suke kai irin munanan hare-haren dake faruwa a Arewa cikin ‘yan kwnakinnan.

 

Gwamnatin tace ciki kuwa hadda harin da aka kai kan jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja.

 

Gwamnatin tace amma tana iya bakin kokarinta waja  magance matsalar ciki kuwa hadda kubutar da wanda ‘yan Bindigar suka sace daga jirgin kasar Kaduna zuwa Abuja.

 

Dama dai dangin wadanda aka sace din sun baiwa gwamnatin tarayya wa’adin awanni 72 na ta kubutar da dangin nasu ko kuma su suyi dukkan mai yiyuwa wajan kubutar dasu.

Karanta wannan  Gwamnonin Najeriya za su ɗaukaka ƙara kan ƙayyade kashe kuɗaɗen ƙananan hukumomi

 

Ministan tsaro, Bashir Salihi Magashi ne ya bayyana haka tare da ministan yada labarai, Alhaji Lai Muhammad yayin ganawa da manema labarai.

 

Sun ce amma fadar abinda gwamnati take yi wajan magance matsalar ga ‘yan jarida bai dace ba, sirrine.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.