fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Tonon Silili: Ji yanda aka gano cewa, kasar Amurka ce ta kashe Ghaddafi dan kada a samu hadin kan kasashen Africa

Rahotanni sun bayyana cewa, an gano wasu bayanan sirri da suka wakana tsakanin tsohuwar wakiliyar kasar Amurka, Hillary Clinton kan kisan tsohon shugaban kasar Libya.

 

An kashe Gaddafi aka kafa gwamnati a kasar Libya bayan zarginsa da take hakkin bil’adama, saidai da yawa sun yi Allah wadai da lamarin.

Tun baya rushewar gwamnatin Ghaddafi dai aka ci gaba da samun masu ikirarin jihadi duka cika kasar inda kusan aka kasa samun tsayayyar gwamnati.

 

An samu Rahotannin cinikin bayi da safarar makamai a Libya wanda suka rika kwarara a kasashen Afrika ana ta ayyukan kisan rayuka dasu.

Karanta wannan  'Yan Bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasa sun ce zasu fara kashesu

 

A duk zaman da ake na kungiyar kasashen Africa, AU Ghaddafi kan yi kokarin kawo maganar hadin kan kasashen Afrika dan samar da hadaddiyar kasar Afrika guds daya.

Saidai bai cika samun goyon baya ba akan hakan.

 

Rahotanni sun nuna cewa, Ghaddafi ya tara kudade masu yawa da suka kai Dala Biliyan 7 dan tabbatar da wannan aniya tasa.

 

Hakane ya tayarwa da kungiyar kasashen yamma hankali inda suka tabbatar da cewa wannan mafarki nashi bai yiyuba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.