fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Tonon Silili: Ji yanda aka raba Miliyan 100 ta kudin fansa da aka kaiwa ‘yan Bindiga da wasu sojojin Najariya

Daya daga cikin mutane 3 da ‘yan Bindigar da suka yi garkuwa da mutanen jirgin kasar dake jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja suka saki jami’in hukumar shige da fici ta kasa ne.

 

‘Yan uwa da abokan arzikin Deji Oyewunmi sun tara Miliyan 100 wadda aka yi amfani da ita wajan biyan kudin fansar da aka sakoshi.

 

Daya daga cikin wadanda suka kai kudin fansar ya bayyanawa jaridar peoplesgazette cewa, kamin su kai wajan da ‘yan Bindigar suke, sun hadu da shingen sojoji da yawa.

 

Yace sojojin sun rika karbar 100,000 zuwa 220,000 daga cikin kudin fansar da zasu kaiwa ‘yan Bindigar.

Karanta wannan  Shugaban sojin Najeriya yace matsalar tsaro ba zata hana ayi zaben shugaban kasa ba a shekarar 2023

 

Yace kuma karara suka rika gaya musu cewa kasonsu ne daga cikin kudin fansar kuma ‘yan Bindigar zasu fahimta.

 

Yace kamin su kai wajan ‘yan Bindigar,  sojojin aun karbi jimullar 700,000 daga cikin kudin.

 

Zuwa yanzu dai hukumar sojin Najariya bata ce komai ba kan wannan zargin da aka musu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.