Ta bayyana cewa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour party wanda yawanci Inyamurai ke goyon baya, Peter Obi ya karbi Biliyoyin Naira a hannun Atiku.
Lamarin ya farune a zaben shekarar 2019 da ya gabata inda kuma akace yayi amfani da kudaden ne wajan sayen kuri’u a lokacin zaben.
Shahararren dan fafutuka, Kwamared Deji Adeyanju ne ya bayyana haka a shafinsa na sada zumunta.
Deji ya bayyana hakane yayin da wani ya zargeshi da karbar kudi a hannun Atiku, ya kuma bayyana cewa tunda yake bai taba karbar ko sisi a hannun Atiku ba amma Peter Obi ya taba.