fbpx
Wednesday, October 21
Shadow

Tottenham 3-3 West Ham: West Ham ta yi abinda ba’a taba yi ba a Premier League

Wasan da West Ham ta rike Tottenham 3-3 ya bada mamaki sosai saboda Tottenham na cin 3-0 har zuwa mintuna 81 amma daga baya da West Ham ta yi zuciya duk sai da ta farke kwallayen.

 

Son ne ya fara ciwa Tottenham kwallayen inda daga baya kuma Harry Kane shima ya ci kayatattun kwallaye 2. Tottenham ta sha wasa ya kare, ta yi nasa amma ana Minti 82 da wasa ta fara ramawa inda duka sai da ta farkesu.

A tarihin gasar Premier League babu kungiyar da aka taba cinta 3-0 har aka kai mintuna 81 da wasa sannan kuma ta ramasu sai West Ham din.

 

Sauran wasannin da aka buga a yau sune, Crystal palace da Brighton wanda aka tashi 1-1, sai Sheffield United da Fulham wanda shima aka tashi 1-1.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *