Luton Town ta yi rashin nasara 1-0 a gida a hannun Tottenham a wasan mako na takwas a Premier League ranar Asabar.
Micky van de Ven ne ya ci kwallon a zagaye na biyu, kuma karon farko da ya ciwa kungiyar kwallo bayan da ya samu tamaula ta wajen James Maddison,
To sai dai, tun kafin nan an bai wa ɗan wasan Tottenham jan kati, Yves Bissouma, inda kungiyar ta Landan ta kare fafatawar da ‘yan kwallo 10 ciki a cikin fili.
Tottenham wadda Ange Postecoglou ke jan ragama ta yi wasa takwas ba tare da an doke ta ba a Premier League da nasara shida da canjaras biyu.
Tuni dai Tottenham ta zama ta ɗaya a teburin Premier da tazarar maki biyu tsakaninta da Manchester City, wadda za ta je gidan Arsenal ranar Lahadi.
Wannan shi ne karon farko da Luton da Tottenham suka kara tun bayan Maris ɗin 1992.
Tottenham ta yi wasa 10 kenan da Luton a bayan nan ba tare da rashin nasara ba, inda rabon da Luton ta doke Tottenham tun Nuwambar 1987.