Gwamnatin tarayya ta zargi kungiyar Malaman Jami’a ta ASUU da son kai wanda tace shine yasa malaman suka tafi yajin aiki.
Karamin ministan Ilimi, Emeka Nwajuiba ne ya bayyana haka inda yace malaman suna batawa yara lokaci.
Yace malaman suna yajin aiki ne akan kudin a karshe dai dun min dadewa za’a biyasu.
Yace kuma duk da yajin aikin da suke, har yanzu ana biyansu Albashinsu.