Ma’aikatan gwamnati da sukayi ritaya a jihar Abia sunyi zanga-zanga a ranar talata kan rashin biyansu fansho na tsawon watanni 38, da kuma gratuti.
Tsaffin ma’aikatan sun bayyana cewa zasu cigaba da yin zanga-zangar domin gwamnati ta biya su albashinsu na watanni 38, da kuma gratuti na tsawon shekaru ashirin.
Shugaban kungiyar, Emeka Okezie ya bayyana cewa kodama an biyaau kashi daya bisa hudu na albashinsu ne ake basu, kuma baya isarsu su biya kudin makarantun yaransu da kuma kuma da kula da lafiyarsu bakidaya.