fbpx
Saturday, August 8
Shadow

Tsaffin shuwagabannin kasa, Obasanjo da Jonathan sun yaba da kokarin hukumomi kan yaki da Coronavirus/COVID-19

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa yana yabawa shuwagabannin Najeriya kan kokarin da suke waja  yaki da cutar Coronavirus/COVID-19.

 

Ya bayyana hakane a wata Gajeruwar hira da aka yi dashi inda aka tambayeshi me zai ce akan cutar Coronavirus/COVID-19 a Najeriya.

Yace yana jinjinawa shuwagabanni daga sama har zuwa kasa sannan kuma yana jinjinawa Ma’aikatan lafiya da suka sadaukar da rayuwarsu wajan shiga gaba-gaba su yaki wannan cuta, kamar yanda Guardian ta ruwaitoshi.

 

Hakanan shima tsohon shugaban ksa, Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana cewa yana jinjinawa musaman gwamnonin saboda kokarin da suke.

 

Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi ta fasahar sadarwar zamani kamar yanda muka jiyo daga The Cable.

 

Jonathan ya kara da cewa abinda ma yake birgeshi da gwamnonin shine yanda suke shiryawa abinda zai faru bayan wucewa cutar Coronavirus/COVID-19.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *