fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Tsaffin shuwagabannin tsaro sun bayyana dalilin da yasa suka kasa Gamawa da Boko Haram inda Buratai yace za’a iya kai shekaru 20 nan gaba ana fama da matsalar

Duka tsaffin shuwagabannin tsaro sun amince cewa an samu yawaitar matsalar rashin tsaro a karkashinsu.

 

Sun amince da hakanne a yayin ganawa da kwamitin dake tantancesu na majalisar Dattijai a matsayin Ambasadojin Najeriya.

 

Tsohon shugaban Hedikwatar tsaro,  Janar Gabriel Olonisakin ya bayyana cewa, babbar matsalar tsaron Najeriya shine dazukan da aka kasa kula dasu.

 

Ya dora alhakin hakan akan Gwamnonin jihohi, inda yace Najeriya nada dazuka 1000 wanda idan ba an rika kula dasu ba to lallau matsalar tsaro zata ci gaba

 

Hakanan shima tsohon shugaban sojojin Najeriya,  Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa, inda ake samun Kuskure shine da mutane ke tunanin Sojojin ne kadai zasu iya maganin wannan matsalar.

 

Yace kuma ba haka bane, Yace sai Gwamnati,  Shuwagabannin Al’umma dana addinai sun saka hannu, an samarwa matasa ayyukan yi an samar da Tituna masu kyau, an bayar da Ilimi. Yace idan ba haka aka samu ba to lallai za’a kai shekaru 20 nan gaba ana fama da wannan matsala.

 

Janar Buratai ya kuma bayyana cewa, akwai garuruwan da babu wata alamar gwamnati a cikinsu wanda irinsu ne ‘yan ta’addar ke amfani dasu suna canjawa mutanen kauyukan tunani dan su goyi bayansu.

“My state (Borno), is an epicentre, where this indoctrination has penetrated so deep. They (insurgents) have won the communities to their side. That is why they (communities) keep Boko Haram. So it is complex, it requires a whole of government approach to solve this, military action or activity is just one aspect.

“One mistake that we have been making is that only the military can solve this. It is not. There are political, social, economic aspects that need to be addressed.

Development should be progressive, there should be roads everywhere, there should be employment, schools and hospitals all over.

“Yesterday, I counted five local government areas in Borno State that do not have good access roads.

“In northwest, north central, there are so many ungovernable spaces, which the insurgents are penetrating. The places don’t have schools, hospitals and so on and education is very fundamental.

“Unless these things are done, this insecurity will continue because the truth must be told. It may take another 20 years for the country to surmount the problem of Insurgency and that is the truth.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *