Tsagerun ‘yan bindiga sunyi garkuwa da matafiya hudu a jihar Anambra ranar lahadi bayan sun babbaka masu motarsu.
‘Yan bindigar sun kai masu farmakin ne a babban birnin jihar wato Awka da rana tsaka wurin misalin karfe uku, kuma babu nisa sosai zuwa gidan gwamnatin jihar da inda abi ya faru.
Amma hukumar ‘yan sanda tace jami’anta sun fara neman ‘yan bindigar domin a hukuntasu kuma a ceto matafiyan da suka kama.