fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Tsakanin Ronaldo da Messi waye ya fara samun damar yin wasa a tawagar yan wasa 11 na farko?

Cristiano Ronaldo da Lionel Messi sun mamaye duniyar wasan kwallon kafa fiye da shekaru goma da suka gabata kuma sun lashe kyautar balloon d’Or har 11 tsakanin su.

Cristiano Ronaldo ya fara buga wasan kwallon kafa a kungiyar Sporting, kuma ya samu damar shiga tawagar yan wasan 11 na farko a kungiyar yayin da yake da shekaru 16 a shekara ta 2002 a watan oktoba. A lokacin Ronaldo yayi nasarar jefa kwallaye biyu a wasan da suka buga da Moreirense na gasar primeira liga. Sun tashi wasan 3:0.
Shi kuma Messi ya samu damar shiga tawagar yan wasan 11 na farko a kungiyar Barcelona a shekara ta 2004 a watan oktoba. Shekaru biyu da kwanakin tara kenan bayan Cristiano Ronaldo ya samu wannan damar. Kuma a wannan lokacin Ronaldo har ya samu damar bugawa Portugal wasa.
Ronaldo ya fara bugawa Portugal wasa a shekara ta 2003 a watan augusta, bayan shekaru biyu shima Messi ya samu damar yiwa Argentina wasa a shekara ta 2005 a watan augusta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.