Hukumar ‘yan sanda a jihar Kaduna tayi nasarar kashe ‘yan bindiga guda biyu a kauyen Kimbi dake karamar hukumar Birnin Gwari.
Mai magana da yawun ‘yan sanda ASP Muhammad Jalinge ne ya tabbatar da hakan a ranar Alhamis, inda yace hukuma ta kwato bindugun biyu a hannunsu na AK47.
Kuma sun jiwa wasu ‘yan bindigar raunika inda ya kara da cewa hukumomi da gwamnati na iya bakin kokarinsu wurin kare rayukan al’umma.