fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Tsaurin ra’ayin addini: An rufe masallaci a Faransa

Gwamnatin Faransa ta bayar da umarnin rufe wani masallaci a Arewacin ƙasar sabo da abin da ta kira tsaurin ra’ayin addini da limamin masallacin ke nunawa a yayin wa’azizzikan sa.

Za a rufe masallacin har tsawon watanni shida, in ji mahukunta.

Masallacin na lardin Beauvais, garin da ya ke da al’umma da ba ta wuce dubu 50 ba a Arewacin birnin Faris.

A takardar da dagacin lardin ya rubutawa mahukuntan Masallacin, gwamnatin ƙasar ta ce huɗubar da limamin yanke yi a yayin sallar Juma’a na haifar da tsana, rikici da kuma kariya ga jihadi.

A watan nan ne wata jaridar Faransa, Courier Picard, ta rawaito cewa limamin bai daɗe da shiga musulunci ba.

Karanta wannan  Mai kudin Duniya, Elon Musk ya sayar da hannun jarinsa na dala biliyan 6.9 na kamfanin Telsa, shin ko meye dalili?

Jaridar ta rawaito lauyan ƙungiyar da ke kula da masallacin na cewa an yi wa limamin mummunar , in da ya ƙara da cewa an dakatar da limamin da ga limanci bayan da dagacin ya rubuta wannan takarda.

Tun a farkon shekarar nan da mu ke bankwana da ita ne dai gwamnatin Faransa ta sanar da fara sa kafar wando ɗaya da guraren addinin musulunci da su ke yaɗa tsaurin ra’ayi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.