Wata tsawa a ranar laraba ta kashe jami’ai uku na hukumar kula da lafiyar titi dake bangaran jihar Ogun.
Ana zargin jami’an sun mutu ne a ofishin su da ke tsohon Ilese Tollgate a karamar hukumar Ijebu ta arewa maso gabas a jihar.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safiyar yau a yayin da jami’an hukumar da abin ya shafa ke shirin tafiya fareti yau.
Ansamu cewa akwai jami’ai sama da 10 a wurin da lamarin ya faru lokacin da tsawa ta fara.
Lokacin da aka tuntubi, Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar, Florence Okpe, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ta ce, “To, an sanar da mu. Amma, kwamandan sashen na, shi ya tafi can don nemo ainihin abin da ya faru.
“Ba zan iya bayar da rahoto ba har sai ya dawo ya ba mu cikakken bayani game da abin da ya faru.”